Fulani: Hanya Daya Tilo Da Za'a Magance Matsaloli A Arewacin Najeriya

Kungiyar matasa ta Fulani makiyaya a Najeriya tace zata ci gaba daba gwamnatin tarayya goyon baya wajen bankado bata gari a kasar, in har hukumomi na neman shawara daga ardodin dake shugabantar al’ummar Fulani.

A wani taron manema labarai da kungiyar matasan Fulani ta Jonde Jam ta kira a birnin Jos, Shugaban kungiyar Alhaji Saidu Maikano ya fara ne da bayyana rashin jin dadin kungiyar, kan yadda ake fadawa rugagen Fulani da sunan hallaka ‘yan ta’adda.

Maikano ya kuma bada shawara ga al'ummar yankunan, da neman gwamnatin tarayya ta bada tallafi ga makiyaya da suka yi asarar dukiyoyinsu, kana da fito da tsari da kudin zasu shiga hannun wadanda ibtila’in ya shafa.

Shugaban Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah, reshen karamar hukumar Bassa a jihar Pilato, Umar Abdullahi Dakare yace rikicin ya kasa kawo karshe, saboda shugabannin dake karban irin wannan tallafi basa ba wadanda suka yi asara.

Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro wanda ke damun daukacin al’ummar kasar, suke kuma neman mafita.

Zainab Babaji ta hada muna wannan rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Fulani: Hanya Daya Tilo Da Za'a Magance Matsaloli A Arewacin Najeriya 2'20"