Tun shekaru shida da suka gabata ne alummomin suka tsinci kansu cikin wasu rigingimun da suka yi sanadiyar salwantar rayuka da gidaje da gonaki da dabbobi da dai wasu dimbin dukiyoyi.
Har yanzu akwai mutane, musamman Agatu da suke gudun hijira.
A wani taron sasantawa da gwamnonin Bunue da Nasarawa suka jagoranta a fadar gwamnatin jihar Benue al'ummomin sun bayyana wasu matakan da zasu dauka domin inganta zumunci da kyakyawan zaman lafiya mai dorewa.
Basaraken gargajiya a bangaren Agatu Musa Ayigege ya jaddada batun samar da tsaro a yankin Agatu ta yadda al'ummarsu zasu koma gidajensu su cigaba da harkokinsu na yau da kullum.
Yace abun da ya faru ya riga ya faru saboda haka sai a nemi zaman lafiya ta yadda wanda zashi noma ba sai ya dauki bindiga ba. Yakamata a cigaba da ba juna hakuri. Yace duk dokokin da aka shimfida masu Agatu su kiyaye nasu su ma Fulani su kiyaye nasu.
Kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Nasarawa ta bakin shugabanta Muhammad Useni tace sun tanadi rajistan duk wani makiyayi da zai yi kiwo a yankin. Yace yarjejeniyar tsakanin Agatu da Fulani idan Allah Ya yarda zata dore. Yace akwai abubuwa da yawa da zasu tsara su tabbata an zauna lafiya. Yace akwai wasu bata gari dake zuwa suna bata masu suna. Zasu kafa masu tsaro su dinga kiyayewa da duk wanda ya shigo cikinsu.
Dangane da daukan makamai Useni yace doka ta hana yin hakan saboda haka yakamata gwamnati ta tashi tsaye ta hana yawo da muggan makamai. Ya kira a kafa jami'an tsaro a yankin Agatu da Nasarawa domin tabbatar da zaman lafiya.
Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom yace al'ummomin su yadda zasu zauna tare domin samun cigaba saboda yaki baya kawo cigaba. Kamata yayi duk lokacin da suka samu wani sabani su nemi hanyoyin warwaresu.
Gwamnan jihar Nasarawa yace saboda rikicin Agatu da Fulani da manoma yaki ci yaki cinyewa ya sa yayi magana da gwamnan Benue su zauna tare da al'ummomin domin a cimma sulhu. Sun zauna sun kuma nuna masu faidar samun sulhu tsakaninsu.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5