PM Lebanon Sa'ad Hariri ya bada sanarwar yayi murabus a yau Asabar, bayan wani jawabi da yayi inda yayi kakkausar suka kan Iran da 'yar kanzaginta kungiyar Hezbollah kan take taken su a Lebanon din da kuma yankin baki daya. Matakin na yin murabus ya biyo bayan tuntuba da yayi da shugabanni Saudiyya a Riyadh, da kuma wata ganawa da babban jam'i a ma'aikatar harkokin wajen Iran Ali Akbar Velayati.
Hariri wadda yayi jawabi ta tashar talabijin ta kasar, bayan da kafofin yada labarai na kasashen Larabawa suka yi hasashen zai dauki irin wannan mataki, bayan kuma da ya kai wasu ziyarce ziyarce a Saudiyya a baya bayan nan, inda ya gana da Yerima Mohammed Salman.
Hariri ya zargi wasu kasashen waje ma'ana Iran, wacce yace bata da niyya mai kyau ga Lebanon, ta haddasa rarrabuwar kawuna a kasar, inda ta kafa kasa cikin kasa.
Tsohon PM yace yanayin da ake ciki a kasar, dai dai yake da lokcinda aka kashe mahaifinsa a shekara 2005 wanda shima ya shugabanci kasar. Kafofin yada labaran yankin suna zargin Hezbollah da laifin kashe mahaifinsa.