‘Yansandan Faransa sun tilasta bude wata babbar matatar mai dake kusa da birnin paris,a yayinda gwamnatin take kara tsananta matakai da take dauka kan kungiyoyin kwadago,gabannin wani muhimmin kuri’a da majalisar dattijan kasar zata kada yau jumma’a,sauye sauye kan harkokin fanshon kasar.
A safiyar jumma’an nan ne ‘yansanda suka kutsa kai cikin matatar mai dake Grandpuits bisa umurnin gwamnati na tilastawa ma’aikata su koma bakin aiki.
Sassan biyu sun kara kuma an bada labarin akalla mutum daya ya jikkata. Ma’aikata sun baje a harabar matatar mai tun kwanaki, suka toshe hanyoyin shiga,wanda ya kara matsalar karancin mai cikin kasar. A yau jumma’a ce ake sa ran majalisar dattijan kasar zata kuri’a kan shirin.