Fiye Da Yara Miliyan 40 Ke Bukatar Abinci Mai Gina Jiki - UNICEF

Wasu Yara a Sansanin 'Yan Gudun Hijra

Wasu Yara a Sansanin 'Yan Gudun Hijra

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, ta yi gargadin cewa miliyoyin yara dake kasashen duniya, masu fama da tashe tashen hankalu suna fuskantar barazanar mutuwa saboda da matsannacin karancin abinci mai gina jiki a cikin kasashensu.

Kasashen sun hada da Najeriya da Sudan ta kudu da Yeamal da kuma kasar Somalia.

A dangane da hakan asusun ya kaddamar da gidauniyar kudi na dalar Amurka Biliyon 3.3 domin taimakawa mutanen da ta yi kiyasin sun kai miliyan 81 wanda daga cikinsu fiye da rabinsu yara ne dake bukatar abinci mai gina jiki da gaggawa.

Jami’in hulda da jama’a, na asusun dake kula da jihohi shida a arewacin Najeriya, Mr. Samuel Kalu, ya ce abun na farko da suke gudanarwa shine za a tantance yara da suke da matsanancin rashin isasshen abinci mai gina jiki bayan haka sai a ciyar da su abinci mai gina jiki.

A dangane da shirin ba da agajin gaggawa, ya ce asusun na bukatar dalar Amurka, miliyan147 domin samar da abinci mai gina jiki ga yara.

Your browser doesn’t support HTML5

Fiye Da Yara Miliyan 40 Ke Bukatar Abinci Mai Gina Jiki - UNICEF) - 3'00"