A karon farko, wani sabon bincike ya nuna cewa rabin mutanen duniya suna amfani da yanar gizo, kamar yadda kungiyar sadarwar zamani ta yanar gizo ta kasa-da-kasa ‘International Telecomunication Union’ ta bayyana.
Sabon rahoton binciken ya tabbatar da cewa zuwa karshen wannan shekarar, za’a samu kimanin sama da mutane billiyan 3.9 da ke amfani da shafin yanar gizo.
Binciken da aka yi amfani da adaddin yawan na’urori da ake shiga shafukan yanargizo da su, suka tabbatar da karuwar yawan hakan a fadin duniya, kuma binciken ya iya gano cewar mafi akasarin masu amfani da wadannan yanar gizo sun fito ne daga kasashe masu tasowa.
Wanda suka kwashe kimanin kashi 80 na yawan masu shiga yanar gizon a duniya, kuma ana kara samun yawaitar amfani da shafin yanar gizon a kasashen masu talauci. A shekarar 2005 ana da yawan kashi 7.7 amma a wannan shekarar ya kai kashi 5.3.
Kungiyar ta ce a Nahiyar Afrika ne a kafi samun ci gaba mai yawa, wanda mutane da dama na amfani da shafukan yanar gizo wajen ilmantar da jama’arsu.
Binciken, ya tabbatar da cewar an samu koma baya a yadda ake amfani da yanar gizon a kasashen Turai, Amurka da kasashen Asiya.