Firayim Ministar Birtaniya Ta Kai Ziyara Kasar Sin

Theresa May Da Firimiya Li Keqiang

Yau Laraba Firayim Ministar Birtaniya, Theresa May, ta sauka a China domin ganawa da hukumomin kasar game da batun bunkasa harkokin kasuwanci da gagarumar kasa mai karfin tattalin arziki a Asiya, gabannin ficewar Britaniyar daga kungiyar tarayyar turai a badi.

A ziyarar tata, ta tsawon kwanaki ukku, May zata fara yada zango ne a birnin Wuhan dake yankin tsakiyar kasar, kafin ta wuce zuwa babban birnin kasar wato Beijing, inda zata gana da Firimiya Li Keqiang.

Firayim Ministar dai tana tare da ‘yan rakiya da suka hada da ‘yan kasuwan Birtaniya har 50 wadanda suka matsu su fadada harkar kasuwanci a kasar ta China wacce tattalin arzikinta shine na biyu a girma a duk fdin duniya.

May zata gana ne da shugaba XI Jinping gobe idan Allah Ya kai mu, kana jibi juma'a ta kammala ziyarar nata a birnin Shanghai.