Firai Ministan Libya Na Zargin Abokin Hamayarsa Da Neman Juyin Mulki

Fayez al-Sharraj yace Janar Khalifa ne sanadiyar rusa matakan da ake bi na siyasa.

Firai Ministan kasar Libya Fayez al-Sarraj, ya ce, abokin hamayyarsa, da suke takaddama kan mulkin kasar, Janar Khalifa Haftar, yana kokarin shirya juyin mulki, domin ya kwace mulkin kasar da karfin tuwo.

A jiya Laraba, Al Sarraja, ya fadawa gidan talbijin na France 24 cewa, "Haftar na mafarkin shiga birnin Tripoli."

Ya kara da cewa, "dole ne, mu yi Allah wadai, da wannan yunkuri na yunkurin kifar da gwamnatin, da aka amince da ita, shi Khalifa Haftar da kan shi ne ya rusa matakan da ake bi na siyasa.

Ba gwamnati ta kasa ba, kuma a shirye muke, don komawa tsarin siyasa idan har aka cika sharrudan da muke so.”

Shi dai Haftar, na jagorantar wata gwamnati ta daban a gabashin Libya, inda dakarunsa, suka rika kai hari akan na gwamnatin Sarraj, tun a watan da ya gabata, wacce majalisar dinkin duniya, ta amince da ita, amma sojojin Sarraj, da kawayensu, sun ki bari a karbe ikon birnin Tripoli.