Firam Minista May, Zata Gana Da Shugaban Kolin Kungiyar Turai

Firam Minista Theresa May zata gana da shugaban kungiyar tarayyar turai a karo na biyu a wannan satin, don kokarin ceto yarjejeniyya ta ballewar Burtaniya daga kungiyar tarayyar Turai.

Firam Ministan Burtaniyya Theresa May, ta koma birnin Brussels yau Alhamis, domin neman amincewa akan yarjejeniyar da bata yi farinjini ba, ta fidda Burtaniyya daga tarayyar Turai, bayan da ta sha da kyar a wata kuri’ar rashin tabbas da aka jefa akanta.

May zata gana da shugabanin kungiyar tarayyar Turai a karo na biyu, a wannan satin don ta kara kokartawa wajen ceto yarjejeniyar ta ballewa daga tarayyar Turai, bayan ta soke wani zaman kada kuri’a na ‘yan majalissar wakilai wanda aka sa-rai sakamakonsa zai yi watsi da yarjejeniyar.

Ya zuwa yanzu, shugabannin kungiyar tarayyar Turai, sun nuna alamun zasu taimakawa Burtaniyya ta wata hanyar, amma kuma sun nuna a fili cewa basu da niyyar sake tattauna batun sharuddan yarjejeniyar, da bangarorin biyu suka yi aiki akai a watannin da suka kwashe suna tattaunawa.

Shugabannin kungiyar tarayyar Turai zasu taru yau Alhamis da gobe Jumma’a don wani taron koli, shugaban kungiyar tarayyar Donald Tusk, yace zasu saurari bayanan May akan batun, kafin su yi tasu ganawar ba tare da ita ba, don su cimma muhimmiyar matsaya.