Firayin Minista Theresa May ta Britaniya ta ce zata tado da damuwarta yau alhamis idan ta gana da shugaba Donald Trump kan yadda Amurka ta fallasa ma kafofin yada labaranta wasu bayanan sirri dangane da binciken harin bam na Manchester.
Firai minister, wadda ta isa birnin Brussels domin taron kolin kasashen kungiyar kawancen tsaron NATO, ta fadawa ‘yan jarida cewa “babban kawancen da Amurka da Britaniya suke da shi kan harkokin tsaro, an gina shi ne bisa harsashin yarda da amincewa da juna. Wani bangaren wannan amana, shine sanin cewa idan aka mika ma daya wani bayanin sirri, ba za a fallasa shi ba.”
Ms. May ta fada kafin ganawarsu cewa, “zan bayyanawa shugaba Trump a fili yau din nan cewa tilas ne bayanan sirri da hukumomin leken asirinmu suka raba ma juna, na sirri ne.”
Kafofin yada labarai sun ce ‘yan sandan dake binciken harin bam din na Manchester, wadanda suka fusata sosai da bayyana wadannan bayanan sirrin, sun daina musanyar bayanai da takwarorinsu na Amurka.”
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambaci wasu majiyoyi na cewa, dakatar da bada bayanai ga ‘yan sandan Amurka, akan harin zai cigaba da kasancewa har sai an sami tabbaci daga gwamnatin Amurka na cewa ba za su kara fallasa wani bayani ba.
Kafofin yada labaran Amurka da dama sun bayyana sunan wanda ya kai harin kunar bakin waken bisa bayanan da suka samu daga jami’an Amurka, tun kafin ma jami’an Britaniya dake binciken su bayyana sunansa ga duniya.