Jiya Talata Farai Ministar Birtaniya Theresa May ta fuskanci babban koma baya bayan da ‘yan Majalisu ciki har da ‘yan aware sama da 100 daga jam’iyyar ta mai mulki, suka ‘ki amicewa da daftarin yarjejeniyar May na ficewa daga kungiyar tarayyar Turai.
Wannan koma baya da gwamnatin ta samu zata mayarwa Birtaniya hannun agogo baya, bayan da ta tsaida ranar 29 ga watan Maris domin ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai.
‘Yan Majalisu 202 ne kawai suka amince da daftarin, yayin da ‘yan Majalisu 432 suka kada kuri’ar kin amicewa. Wannan koma baya da aka samu ana kwatanta shi da wani irinsa da aka taba samu a baya tun shekarar alif 924, lokacin da Farai Minista Ramsay MacDonald ya sha kaye a kuri’ar da aka kada da 166, lamarin da ya haddasa rugujewar gwamnatinsa da kuma babban zaben da ya sha kaye.
Bayan da aka kada kuri’ar May ta yi kukan cewa zaben bai nuna musu komai ba, akan abububwan da zasu amince akan ficewar Burtaniya da tarayyar Turai.