Firai Ministan Lesotho Ya Fara Gudanar Da Aiki a Rana Ta Farko

Moeketsi Majoro

Firai Ministan Lesotho, Moeketsi Majoro, ya fara gudanar da aiki a rana ta farko a yau Alhamis, kwana daya bayan da ya sha rantsuwar kama aiki a fadar sa a Maseru, babban birnin kasar.

Majoro, dan shekaru 59 da haihuwa kuma tsohon ministan kudi, ya ce abin da zai fi maida hankali shine kare kasar yayin da ake fama da annobar COVID-19 kana da maganace talauci da rashin aikin yi a 'yar karamar kasar da Afirka ta Kudu ta kewaye ta.

Har ila yau, Majoro yana fatan dawo da kwanciyar hanakali a Lesotho, wadda ke cikin rashin zaman lafiya sanadiyyar matsaloli wanda ya gada.

Majoro ya maye gurbin Thomas Thobane mai shekaru 80, wanda yayi murabus na ba zata a ranar Talata, bayan shafe watanni yana shanye matsin lamba daga gwamantin hadin gwiwa da ya sauka saboda zargin yana da hannu a kisan tsohuwar matarsa, Lipolelo Thobane a 2017, ‘yan kwanaki kafin a rantsar da shi.

A wajen bikin rantsar da Majoro, Thobane wanda ya musanta hannu a kisan tsohuwar matartasa, ya kuma nemi afuwar kura-kuran da yayi a tsawon shekaru uku na zamansa Firai Minsta.