Firai Ministan Japan ya gargadi China ta kare rayuka da kaddarorin al'umarsa

Masu zanga zanga a kofar ofishin jakadancin Japan

Firai Ministan kasar Japan Yoshihiko Noda ya yi kira ga China ta tabbatar da kare lafiyar al’ummar kasar Japan da cibiyoyin kasuwancinsu a China, yayinda aka shiga kwana na biyu ana zanga zangar nuna kin jinin Japan a China.

An fara zanga zangar ne sakamakon matakin da Japan ta dauka na mallakar tsibirai dake tekun gabashin China da ake takaddama a kai.

Dubban mutanen kasar China suka yi zanga zanga a kofar ofishin jakadancin Japan dake birnin Beijing jiya asabar, inda suka rika jifa da duwatsu suka kuma kona tutocin kasar Japan. Zanga zangar ta bazu zuwa biranen kasar China da dama.

Wannan tarzomar ita ce ta baya bayan nan a jerin zanga zanga da aka fara gudanarwa tun ranar Talata bayan da Japan tace ta sayi tsibiran daga hannun wanda ya mallake su. China tace wannan cinikin biri a sama ne, yayinda take ikirarin mallakar yankin.

Rikicin ya yi zafi ranar jumma’a lokacin da China ta tura jiragen sa ido shida, suka yiwa tsibiran da ba wanda ke zaune a wurin da ake kira Diayu dake kasar China da kuma Senkaku dake kasar Japan kawanya.