Firai Minista Boris Johnson Ya Nemi A Gudanar Da Zabe

Firai Ministan Birtanoya Boris Johnson yana jawabi a majalisar akilan kasar

A jiya Alhamis Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson, da ke fuskantar kalubale a kokarinsa na ganin Birtaniyya ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai nan da mako mai zuwa, ya yi kiran da a gudanar da zabe da wuri-wuri a ranar 12 ga Disamba.

Johnson ya yi kiran zaben ne don a cewarsa a bai wa masu jefa kuri'a damar bayyana ra’ayinsu kan rikicin ficewar Birtaniyar daga tarayyar ta turai, wanda ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa a majalisar dokoki kasar.

Sai da Johnson na bukatar kashi biyu bisa uku na adadin kuri’un majalisar ta wakilai idan har yana son a amince da bukatar da ya gabatar ta yin zabe da wuri, yayin da babu wata alama da ke nuna cewa akwai yiwuwar zai samu goyon baya.

Yayin da ‘yan jam’iyyar Conservative ke da kasa da rabin kujerun majalisar, Johnson na bukatar gagarumin goyon baya daga jam’iayyar adawa ta Labor.

Sai dai ‘yan jam’iyyar ta Labor, sun ce idan dai har Firai Ministan na son su goyi bayan a gudanar da zabe da wuri, to sai an ba su tabbacin cewa za a jingine batun ficewar kasar daga tarayyar turai a mako mai zuwa - batun da ya Johnson din ya kwallafa rai akai.