Fina Finai Na Daga Cikin Muhimman Hanyoyin Yada Harshe Da Al’ada

A shirinmu na nishadi a yau DandalinVOA ya karbi bakoncin Farfesa Yusuf Adamu, farfesa a bangaren muhalli da ke koyarwa a Jami’ar Bayero ta Kano, yana da kuma sha’awa a harka ta fina finai na tsawon lokaci.

Farfesa Adamu Yusuf, dai ya ce sha’awa ce ta jashi ga harkar ta fim tun 1990, inda ya faro daga rubuce-rubuce a wancan lokaci har ta kai shi ma ga fitowa a matsayin jarumi a wasu daga cikin fina-finan wancan lokaci.

Ya ce daga cikin matsalolin da masana’antar fim ke fuskanta a yanzu, ya ta’alaka ne mafi yawa daga bangaren rubutun fina-finan, wanda a yanzu kowanne mai sha’awa na iya shiga harkar ta fim, kuma hakan ya haifar da rashin bincike kafin a kai ga rubuta fim.

Farfesa ya ce fina-finai a yanzu ko dai a ce rubutun labarin basa samun cikakken bincike, ko kuma bayan an rubuta su akan samu sauyi wajen aiwatar da shi, ya kara da cewa fim na daya daga cikin muhimman hanyoyin yada harshe da al’ada, wanda aka rasa hakan a fina-finan yanzu.

Daga cikin matsalolin kamar yadda yake cewa, sun faro ne daga gundarin labari, wanda idan aka yi la’akari da fina-finan yanzu suna sauka daga labaran kasar Hausa, zuwa aro na wasu al’adu, kamar na India ko al’ada irin ta Turawa, wasu lokutan ma har a dangana da labaran na Nijeriya wato da 'yan kudu a matsayin labarin Hausawa.

Akwai bukatar masu shirya fim su maida hankali wajen inganta labarai na kasar Hausa, tare da samun wadanda zasu fito a fina-finan su tare da dai-daitaciyar Hausa, da ke bambance jinsin mace da na namiji.

Farfesan dai ya ce ko a yanzu ya shafe shekaru da dama yana rubuta wani fim mai sunan 'Tsinuwar Ganuwar Kano' wanda Wambai yayi. Kuma yake binciken labarin har kawo yanzu kan fim din kafin ya kai ga fito da shi.

Your browser doesn’t support HTML5

Fim Na Daya Daga Cikin Muhimman Hanyoyin Yada Harshe Da Al’ada 7'18"