A Shirin mu na Bollywood, na wannan makon mun binciko fina finai goma da ake sa ran cewa zasu yi fice a wannan shekarar ta 2017, ne.
Amma a wanna makon zamu fara ne da fim din Kaabil, shi dai wanna wani fim ne na soyayya wanda Vijay Kumar Mishra ya rubuta, shi kuwa Sanjay Gupta ya bada umarni inda Rakesh Roshan shi ya kasance producer a karkashen kamfanin FilmKraft.
Wannan film din kamar yadda muka sheda maku kimanin makoni ukku da suka wuce fim ne na makafi biyu wadanda daga bisani suka tsunduma ciki soyayya, babu kama hannun yaro, an kuma jima ana batun wannan fim din, amma masu hikimar Magana na cewa gani ya kori ji.
Rajesh Roshan, shi ya kasance mai daukar nauyin sauti fim din abinda ke nuni da cewa kwararru ne aka hada a wurin hada wanna fim din mai suna Kaabal.
Shi dai fim din Kaabal, da wasu kamar Tamil da Telugu, a ranar 25, ga watan nan na Janairu, ne za’a fitar dasu a gidan sinima a Indiya.
Sanjay Gupta, ne ya bayana fitar fim din Kaabal, a hukumance a watan Janairun shekarar da ta gabata, inda ya bayana cewa Rakesh Roshan, zai kasance fitatcen jarumi a ciki.
Ya kuma kara da cewa an fara daukar hoton wanna fim din ne a watan Maris, na shekara da ta gabata a birnin Mumbai, in da aka kammala daukar shi a watan Yuli, na shekarar 2016, da ta gabata, an kwashe kwanaki saba’in da bakwai ( 77), wajan daukar fim din har karshe. Shi dai wannan fim din sai wanda ya gani.
Your browser doesn’t support HTML5