Hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA, tace babu wani alamu dake nuni da cewa batun da ake yi na shaye-shayen kwayar kara kuzari a faggen wasanin motsa jiki ya shafin wasan kwallon kafa a kasar Rasha.
FIFA, tace ta sa ido sosai akan batun shaye-shayen kwayar da hadin gwiwar hukumar dake kula da shaye-shayen kwayar kara kuzari,na duniya, a tsakanin ‘yan wasa.
A laraban da ta wuce kafofin yada labarai na Jamus da Faransa, suka yada cewa akwai alamun shan kwaya mai kara kuzari tsakanin, ‘yan wasa da aka danganta shi wani dakin gwaje-gwaje na kasar Rasha.
FIFA, tace ta na son amfani da dakin gwaje-gwaje na kasar Rasha, domin gwada ‘yan wasa a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za’a yi a shekara 2018, da kuma gasar Confederation Cup, na shekaran 2017.