A yau Litinin, hukumar kwallon kafa ta FIFA, ta harmatawa jami'in da ta damkawa ragamar duba 'yan takarar da suka nemi daukan nauyin gasar cin kwallon kafa ta shekarar 2018 da kuma 2022, yin mu'amulla da wasannin kwallon kafa na tsawon shekaru bakwai bayan da aka same shi da laifin kin bin ka'ida.
kwamitin da ke kula da ka'idojin hukumar ta FIFA bai fito karara ya bayyana matsayar da ya dauka na dakatar da Harold Mayne Nicholls ba, wanda ya kasance tsohon shugaban kwallon kafa na kasar Chile.
Yanzu haka Mr. Mayne-Nicholls ya na kalubalantar wannan matsaya da aka dauka a kan sa, inda ya yi zargin cewa ba a bashi dama ya kare kansa a baina jama'a ba, yana mai cewa zai kalubalaci wannan hukuncin a kotu. A baya, Mr. Mayne- Nicholls dai yana da burin ya tsaya takarar neman shugabancin hukumar ta FIFA a daidai lokacin da kwamitin ya ta da wannan na rashin bin ka'ida.
A shekarar 2010 ne aka nada Mayne- Nicholls a matsayin shugaban wani kwamiti mai dauke da mambobi shida domin yin nazarin wadanda ke da sha'awar daukar nauyin gasar cin kofin duniya ta 2018 da kuma 2022.