Hukumar dake kula da wasan kwallon kafa ta Duniya (FIFA), ta bayyana sanarwar biyan wasu makudan kudade na alawus da ya kai dalar Amurka miliyan $209, ga kungiyoyin kwallon kafar da suka baiwa 'yan wasansu damar halartar gasar cin kofin duniya na bana 2018, da ya gudana a kasar Rasha inda suka wakilci kasashensu.
Akalla kungiyoyin kwallon kafa 416 daga kasashe 63 za su amfana da kudaden, kamar yadda FIFA ta bayyana.
Kowanne dan wasa daga cikin su dari 736 da suka halarci gasar cin kofin duniyar zai samu kaso na dala dubu $8,530.
Cikin kungiyoyin, Manchester City ta kasar Ingila, ita ke kan gaba na samu kaso mafi tsoka ta dala miliyan biyar da doriya, sauran kungiyoyin su biyo ta a baya.
Kaso mafi tsoka na dala miliyan $158 daga cikin dala miliyan $209 da FIFA ta bayar, ya tafi ne hannun kungiyoyin kasashen Turai.