WASHINGTON, DC: —
Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles a Najeriya ba ta matsa mataki na gaba ba, a cikin jerin matsayi da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar a jiya Alhamis, inda kasar ta ke mataki na 31 a watan Fabrairun 2020.
Rahoton da FIFA ta fitar a 2019 ma ya nuna Najeriya ta na a wannan matsayin ne 31 a cikin jerin kasashen Afirka.
Najeriya tana mataki na uku cikin wadanda su kafi kyau a nahiyar, tana bayan Senegal da Tunisia, su kuwa Algeria da Morocco sun kasance cikin matsayi na biyar.
Senegal ta ci gaba da kasancewa cikin gasar zakarun nahiyar Afirka, inda ta ke da maki 1555, wanda ya kai ta ga mataki na 20 a duniya, ita kuwa Tunisia ta na mataki na 27 a duniya.