Ficewar Birtaniya a EU: Kallo Ya Koma Majalisar Wakilai

Firai Ministan Birtaniya Boris Johnson (tsakiya) tare da wasu kusoshin nahiyar turai a wani taro da suka yi a Brussels. APTOPIX Belgium EU Brexit

Shugabannin Tarayyar Turai suna fatan majalisar dokokin Birtaniya za ta kada kuri'ar amincewa da sabuwar yarjejeniyar ficewa daga tarayyar turai idan ta zo gaban 'yan majalisar a gobe Asabar, amma tuni jam’iyyun adawa suka ce ba za su amince ba.

Firai Minista Boris Johnson da kungiyar tarayyar turai sun cimma matsaya a safiyar jiya Alhamis, makonni biyu kafin alkawarin da ya yi na ficewa daga tarayyar turai, ko da yarjejeniyar ko babu.

Johnson ya kira sabuwar yarjejeniyar "mai girma" ga Birtaniya, da mutanenta, da kungiyar tarayyar turai.

Sai dai dukkanin jam’iyyun adawar kasar, sun yi fatali da yarjejeniyar ciki har da kawayen Firai Minista Johnson, Northern Ireland Democratic Unionist Movement.