Hukumar FBI tana cigaba da binciken wani tafki a birnin San Bernardino inda maharan suka je bayan sun kashe mutane 14 da jikata wasu 21 kuma ana kyautata zaton nan ne suka jefa kwamfutarsu domin batar da shaida
A jihar California, kwararrun nunkaya suna aiki a tabki a birnin San Bernadino, inda aka bada rahotannin cewa mata da mijin nan wadanda suka kashe mutane 14 makon jiya, aka gansu sunje wurin a ranar da suka karkashe mutanen.
Mukaddashin darektan FBI mai kula da shiyyar Los Angeles, David Bowdich, yaki yayi bayanin aininhin me masu nunkayan suke bida a cikin tafkin jiya Alhamis.Amma wata kafar yada labarai tace sai tayu akwai kundin na'urar komputa da watakil ake zargin maharan suka jefa a ciki.
Bowdich, yace bincike a tafkin zai dauki kwanaki. Yace hukumar zata gasa a aikinta idan ta kasa binciken duk wani bayani data samu.