Wadanda suka kai harin jiya Litinin sun ce su magoya bayan ISIS ne
WASHINGTON, DC —
Hukumar FBI tana binciken hari ta yanar gizo da aka kai kan Twitter da You Tube da babbar hadaddiyar cibiyar kwamandojin Amurka dake kula da hare-haren jiragen sama akan kungiyar ISIS dake kasashen Iraqi da Syria.
Wadanda suka kai harin jiya Litinin sun ce su magoya bayan ISIS ne kuma suna yiwa sojojin Amurka barazana. Sun kara da cewa “Muna zuwa. Ku yi hattara. ISIS”
Maharan sun samu wasu bayanai da suka hada da lambobin wayar tarho da adireshi na email da na gidajen daruruwan jami’an sojojin Amurka.
Maharan sun kuma samu hotunan kasashen China da na Koriya ta Arewa.
To saidai cibiyar kwamandojin tace maharan basu samu bayanai kan shirye-shiryenta ba ko kuma wasu bayanan asiri