Masana na cigaba da yin fashin baki game da yarjajjeniyar da Najeriya da China su ka cimma na musanyar takardun kudadensu kai tsaye, a wani yinkurin Najeriya na farfado da darajar Naira, wadda ta fadi.
Masanin tattalin arziki Dokta Dauda Muhammed na Jami’ar Ado Bayero ta Kano, ya gaya ma wakilinmu a Lagos Babangida Jibrin cewa wannan yarjajjeniyar, wadda ake kira “Currency Swap” a Turance, na nufin cewa za a rinka samun kudin China kai tsaye ba tare da an yi amfani da dala a matsayin ma’aunin darajar Naira ba. Dokta Dauda ya ce sannu a hankali darajar Naira za ta farfado saboda bukatar dala za ta ragu tsakanin ‘yan kasuwan Najeriya. Wani dankasuwa a birnin Lagos mai suna Chika Chikodi ya ce lallai wannan matakin zai taimaka wajen farfado da darajar Naira.
Haka zalika, wani masanin tattalin arziki mai suna Dokta Ahmed Adamu ya gaya ma Ibrahim Ka-Almasih Garba cewa, wannan matakin zai taimaki Naira na wani dan lokaci, to amma ya kamata a kuma dau matakai daga tushe na karfafa Naira saboda nan gaba ma darajar kudin China za ta karu ta yadda takardar kudin China za ta yi tsada kamar yadda ta dala ta yi.
Ga cikakken rahoto daga Babangida da kuma karshen hirarr Ka-Almasih Garba da Dokta Ahmed Adamu:
Your browser doesn’t support HTML5
Your browser doesn’t support HTML5