Rahotanni daga jamhuriyar Nijer sun ce wani abu ya fashe a unguwar Tudu dake garin Agadez yayin da yara almajirai 12 ke kewaye da shi, kuma ya yi sanadiyar mutuwar daya daga cikin almajiran yayin da sauran su 11 suka jikkata, daya daga cikin su na cikin matsananci hali.
WASHINGTON D C —
Gwamnan jihar Agadez ya isa wurin da lamarin ya faru kuma ya je babban asibitin jihar domin ganin halin da wadanda suka jikkata suke ciki.
Madame Hajiya Alzuma, ita ce mataimakiyar magatakardan gwamnan jihar Agadez, a lokacin ziyarar ta bayyana yadda lamarin ya faru.
Adamu Hudu, malamin yaran almajiran da wannan ittila'in ya rutsa da su ya ce karar da ji ta sa ya fita waje ya ga yaran a cikin mummunan yanayi.
Jami’an kwana - kwana su ne su ka kai agaji a lokacin da wannan abu ya faru kuma shugaban su Lieutenant Taro Mahamadu ya ce bututun iskar gas na dafuwa ne ya fashe,
Haka kuma hukumomi sun tabbatar da cewa ba bom ne ba kuma ba wani makamin yaki bane.
Ga karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5