Fashewar Bututun Mai Ta Halaka Mutane Da Dama a Bayelsa

Wani yanki a garin Fatakwal da aka shimfida bututan mai a yankin Niger Delta na Najeriya

Mutane da dama ne ake tararrabin sun mutu, bayan da wani bututun mai ya fashe a kudancin Najeriya a cewar hukumomin kasar.

Ajiya Asabar, Kamfanin Dillancin Labarai na Associated a Press ko kuma AP a takaice, ya ruwaito cewa sama da mutum 50 sun bata, kwana guda bayan fashewar, wacce ta auku a yankin ruwan da ake kira Nembe a jihar Bayelsa.

Kamfanin Aiteo, wanda shi ke da mallakin bututun man, ya ce babu wanda ya rasa ransa a hadarin.

Sai dai wani mai magana da yawun al’umomin yankin, Cif Nengi James- Eriworia, ya fadawa manema labarai cewa, mutane da dama, ciki har da kananan yara sun bata.

Ya kara da cewa, hayakin da ya tashi daga fashewar, ya gurbata iska da ruwan yankin da ake ayyukan su, yana mai kira ga gwamnatin Najeriya da ta kawo dauki tare da gudanar da bincike.

Kamfanin na Aiteo, ya bayyana cewa wutar ta tashi ne da misalin karfe hudu na safiyar ranar Juma’a, amma ba a samu shawo kanta ba, sai ranar Asabar, inda ya ce, babu wanda ya mutu.

Amma, Cif James ya musanta wannan ikrarin da kamfanin ya yi, inda ya ce, har yanzu wutar na ci gaba da ci, kuma akwai fargabar cewa ta rutsa da mutane da dama.