Fashewar ta faru ne a wata mahaka mai zaman kanta dake garin Laisu da safiyar jiya litinin, a cewar kamfanin dillancin labaran Xinhua.
Mataimakin magajin garin Chongqing ya fadi cewa an kaddamar da shirin neman mahakan da suka bata, ko da yake kokarin aikin ceton na fuskantar cikas saboda baruguzan da fashewar ta haddasa da kuma ganin iskar gas ta gurbata wurin da guba.
Hukumomi sun riga sun kaddamar da bincike akan mummunar fashewar kuma jami’an yankin sun bada umurnin dakatar da aiki a kananan mahakun dake yankin na dan lokaci.
A farkon shekarar nan, kamfanin dillancin labaran Xinhua ya ce hukumar kula da harkokin magashin kasar China ta ce, an sami hadarurrukan gas guda 171 a mahakun kwal guda 45 a shekarar da ta gabata.