Fari a Yankin Somaliland Na Barazana Ga Mutane Da Yawa

Kwamitin kula da ‘yan gudun hijira na kasar Norway da ake kira NRC a takaice ya fadi cewa ta yiwu a ci gaba da fuskantar kalubalen fari a yankin Somaliland dake Afrika, abinda zai jefa mutane dubu dari bakwai da ashirin da biyar cikin barazanar yunwa.

“Dubban mutane, musamman mata da yara, wadanda dama basu da isasshen abinci na fargaban yanayin su zai kara tsananta a yayinda ake hasashen ba za a sami ruwan sama ba nan da watanni masu zuwa, a cewar Victor Moses, shugaban kwamitin na NRC a Somaliland.

Somaliland, yankin da ke cin gashin kansa daga Somaliya, na fuskantar kalubalen fari lokuta da yawa ga kuma rikice-rikice da suka addabi yankin Sool.

Moses ya yi kira ga kasashen duniya akan su taimaka da dala biliyan 1.8 don ci gaba da gudanar da ayyukan agaji a yankin.

Idan ba a sami wadannan kudaden ba, Moses ya ce, za a sami hasara sosai, ta bangaren tattalin arziki da kuma yawan mutanen da za a rasa.