Farfasa Yemi Osinbajo da APC ta amince ya zama mataimakin Janaral Buhari wani shehun malami a fannin shari'a. Bayan da ya samu digiri din shi na farko a Jami'ar Legas yayi karatun digiri na biyu da digirgir a London School of Economics dake Birtaniya.
Ya yiwa tsohon gwamnan jihar Legas kuma shugaban APC na yanzu Bola Ahmed Tinubu kwamishanan shari'a har na tsawon shekaru takwas.A cikin shekarun ya kawo canje canje da dama da suka inganta jihar Legas a fannonin shari'a, tattalin arziki, da'a da tabbatar da adalci a shugabanci.
Farfasa Osinbajo limamin mijami'ar Redeem ne inda yake aikin ibada tare da taimakawa wurin horas da sabbin fastoci.
Yayi fice a fannin shari'a dake kula da kiyaye dokoki da yin da'a a harkokin kasuwanci da cinikayya. Akan wannan fanni ne ma yake baiwa bankin raya kasa na kasashen Afirka shawara. Yana kuma cikin daraktocin Citibank.
Farfasa Osinbajo yayi aiki a fannoni daban-daban na Majalisar Dinkin Duniya kana kuma babban lauya ne a tsarin kotun Najeriya da kamfanin lauyoyi da yayi fice a duniya da aka sani da suna Simmons-Cooper.
Ya wallafa littafai da dama kuma yana daya daga cikin wadanda suka kafa hukumar tabbatar da mutunci da gaskiya a harkokin kasuwanci.
Wadanda suka san Farfasa Osinbajo sun ce kamar Janaral Buhari, mutum ne mai tsare gaskiya ko menene ma zai faru.