Jiya Laraba Mukaddashin shugaban kasar Najeriya Farfasa Yemi Osinbajo ya yi ganawa ta musamman da duk shugabannin jam'iyyarsu daga jihohin kasar 36.
A cewar Mr. Ajomale na jihar Legas sun tattauna ne akan abubwan dake faruwa cikin kasar tare da rashin lafiyar shugaban kasa wanda a yanzu yake jinya a Ingila.
Babban sakataren jam'iyyar na kasa Alhaji Mai Mala Buni yayi karin bayani akan muhimman abubuwan da aka tattauna a taron.
Yana mai cewa ganawar tamkar ziyarar ban girma ce ga Mukaddashin Shugaban kasar inda suka tattauna abubuwan da suka shafi jam'iyyar a jihohinsu. Sun bayyana fatan alheri da suke yi masa tare da shugaban kasa.Sun yi fatan Allah Ya dawo dashi lafiya kana sun jinjinawa Mukaddashin.
Ya kara da cewa nan ba da dadewa ba ana kyautata zaton dawowar shugaban saboda wai shugaban ya mulmule yana jiran likitocinsa ne kawai su sallameshi. Yace babu wani abu mai zafi da za'a yi harsashen ko an yi wata magana ta musamman.
Har yanzu dai ba'a ce ga lokaci ko ranar da Shugaba Muhammad Buhari zai dawo ba.
Ga rahoton Umar Faruk Musa .
Your browser doesn’t support HTML5