Rahotanni na nuna cewar farashin danyen mai ya tashi a kasuwar mai ta duniya, sakamakon kisan da kasar Amurka ta yi wa babban jami'in sojan kasar Iran, Qasseem Soleimani. Farashin danyen mai dai yanzu ya tashi da kusan Dalar Amurka uku, inda kowace ganga daya ta haura dala $69.16. Kawo yanzu masu sharhi kan al'amuran yau da kullum na duniya sun yi gargadin cewar wannan matsalar za ta iya haifar da fargaba a Yankin Ta Gabas ta Tsakiya, tare da kawo cikas ga batun samar da man fetur a fadin duniya, wakilinmu na yankin Naija Delta Lamido Abubakar, ya tattauna da Idris Mikati wani mai sharhi kan al'amurran yau da kullum na duniya a Gabas Ta Tsaya, wanda ya lura cewa a duk lokacin da aka samu tashin hankali irin wannan farashin man kan tashi saboda tsaron abin da ne iya biyo baya.
Mikati ya ce akwai fargabatar cewa idan aka fara yaki, jiragen dakon mai ba za su iya jigilar mai daga Gabas Ta Tsakiya zuwa yammacin duniya ba. Wannan shi ya sa mai ya fara tsada, in ji shi.
Ya ce kodayake bai dace b aka yi murna saboda wani bala’in da ya abka ma wasu mutane zai amfane ka, a bayyane ta ke cewa rigimar Amurka da Iran za ta amfani Najeriya ta fuskar tattalin arziki.
Ga wakilinmu a yankin Naija Delta da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5