Farashin Mai: Hadiman Buhari Da Wasu 'Yan Najeriya Sun Yi Allah Wadai Da Wa'adin Kungiyar Kwadago

  • Ibrahim Garba

Wata zanga-zangar kungiyar kwadago a Najeriya

Yayin da ake cigaba da cecekuce kan karin farashin mai a Najeriya, wasu Hadiman Shugaban Najeriya da wasu magoya baya sun yi watsi da matsayin kungiyar kwadago, waddda ta ba da wa'adin tafiya yajin aiki.

Yayin da kungiyar kwadago a Najeriya ke dibarwa gwamnatin kasar wa’adin zuwa daren Talata da ta janye Karin farashin mai da kuma maida tallafin da ta janye a makon jiya, yanzu haka yan Najeriya da kuma hadiman shugaban kasa Buhari, sun shiga maida martani ga wannan barazana ta yan kwadagon, inda wasu talakawa a jihohin Adamawa da Taraba ke ganin da wata manufa kungiyar kwadagon ta dauki wannan mataki, yayin da wasu masu ruwa da tsaki a harkar mai ke ganin itama gwamnati da nata laifin, a cewar wakilnmu a Adamawa Ibrahim Abdula’ziz.

Ibrahim ya ruwaito wani magoyin bayan matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na kara farashin man, wanda bai bayyana sunasa ba, na cewa kungiyar kwadagon ta ki yin zanga-zanga kan rashin biyan albashi da wasu jahohi su ka yi bayan kuwa sun amso kudade daga gwamnatin Tarayya da sunan shirin biyan albashin. Ya ce a baya ma an yi ta fama da karancin man amma su ka ki yin wani abu. Haka ma mutum na biye, wanda ya ce karin farashin man da aka yi ya sa man ya wadata a gidajen mai.

Wani hadimin Shugaban kasa Ibrahim Bafatel Hassan y ace idan ‘yan kasa su ka bayar da hadin kai to za a ci ribar wannan matakin da aka dauka na kara farashin mai. Ya ce abin da ya kamata kungiyar kwadagon ta yi shi ne goyon bayan gwamnati ganin irin matakan kyautata rayuwar jama’a da ta dauka. To amma wani dan kungiyar dillalan man fetur mai suna Alhaji Babakano Jada y ace shi ya na ganin ba wai cire tallafi ya jawo matsalar ba, an kara farashin man ne kai kai tsaye.

Ga Ibrahim Abdulaziz da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Farashin Mai: Hadiman Buhari Da Wasu 'Yan Najeriya Sun Yi Allah Wadai Da Wa'adin Kungiya Kwadago- 3'49''