Hukumar Alhazai ta Janhuriyar Nijar ta fito da farashin kujerar hajjin bana, inda kudin ya tashi miliyan 2 da jaka 276 na Cefa sabanin shekarar da ta gabata inda masu neman tafiya aikin hajjin suka biya miliyan biyu da jaka 238.
Jibril Bukari shine shugaban hukumar alhazai ta janhuriyyar Nijar wato KOHO, yayi bayani cewa kasar saudiyya ta saka ka'idoiji da yawa inda ciki harda kara kudaden abubuwa da yawa, da biyan kashi5 cikin 100 na duk wani kudi da ka biya kuma akwai kudade da suka karu da dama don haka ne kudin ya karu.
A ranar 1 ga watan Mayu na wannan shekarar ne hukumar zata rufe karbar kudaden maniyyata aikin hajji. Jama'a a birnin konni sun nuna rashin jin dadin su akan karin da aka samu, inda suka ce duk shekara sai an kara kudi, sun kuma yi kira ga hukuar da ta lura da hakkin talakawa domin suna shan wahala sosai kafin su hada kudin tafiya.
Shugaban hukumar Alhazai ta Janhuriyyar Jibrin Bukari yayi kira ga al'ummar kasar da su basu hannu domin kallon kaidojin aikin hajjin wannan shekarar, ya kuma yi kira da su dubi kafafen yada labarai domin ganin abubuwa akan aikin hajjin.
Ga rahoto nan a kan rashin jin dadi da yan Nijar a Birnin Konni suka nuna bayan da hukumar alahazan Nijar KOHO ta bayyana kudin kujera hajjin baba a kan Milliyon 2 da jikka 276 inda aka samu karin jikka 38 bisa ga bara.