Binciken da Muryar Amurka ta yi, ya gano cewa, a kasa kamar Najeriya da ta dogara kan kayan kasashen waje 'yan kasuwa na alakanta tashin farashin kaya da tashin farashin dalar Amurka.
A duk lokacin da farashin dala ya sauka kamar yadda yake faruwa yanzu ya kamata a ce farashin kaya ma ya sauka a cewar masu lura da al'amura.
Sai dai hakan ba kasafai ya ke faru wa ba.
Masanin tattalin arziki Abubakar Ali ya ce a zahiri ba za'a ga faduwar farashin kaya ba yanzu saboda kayan dake cikin kasar yanzu wadanda aka shigo da su ne kafin faduwar farashin dalar.
Sai dai ya ce idan an samu dogon lokaci farashin dala na sauka za'a samu canji a farashin kaya.
Alhaji Isa Sakatare daya cikin shugabannin kungiyoyin 'yan kasuwa ya jaddada matsayar da Abubakar Ali ya dauka inda ya ce mutane ba za su samu saukin kaya ba nan take duk da karuwar darajar Naira saboda kayan da suka sayo can baya da tsada ba su kare ba.
Can baya akwai lokacin da aka sayi dalar Amurka fiye da Naira 500 maimakon yadda ake sayenta yau akan Naira 430 a kuma sayar Naira 435
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5