Kafin ma a kara kudin mai, tun lokacin da aka hana shigo da shinkafa ta kan iyakokin kasa farashinta ya tashi daga dubu takwas zuwa goma kana karin kudin mai ya sa ta tashi zuwa dubu goma sha biyar ko fiye ma.
Shugaban 'yan kasuwan arewacin Najeriya Alhaji Ayuba Mohammed yace tunda aka hana shigo da shinkafa ta kan iyaka kamata ya yi gwamnati ta bude iyakokin ta bar wadanda suke da shinkafar su biya kudin kwastan kana su shigo da ita. Abu na biyu yace manyan 'yan kasuwa da suke shigo da shinkafa ta jiragen ruwa sunce basu kara farashi ba.
Alhaji Abubakar Ali wani kwararre akan tattalin arziki yace karin kudin man fetur da aka yi dole ya shafi harkokin sufuri. Dole farashen dauko kaya daga koina ya hau shi kuma dan kasuwa sai ya kara nashi farashin.
Saidai hatta kayan abincin da ake nomawa a cikin gida farashinsu ya tashi. Mansur Isyaka mai tattasai yayi bayanin farashin shinkafa da ake sarafawa cikin gida. Yace farashinta ya tashi daga dubu ishirin da biyu zuwa dubu ishirin da tara haka ma wake.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5