Gwamnati ta yanke shawarar shiga kasuwar musayar kudi ta yin anfani da Babban Banki a karkashin wani tsari inda bankin zai dinga bada dalar Amurka ga bankunan kasuwanci.
Su bankunan an bukacesu su dinga sayar da dalar wa rukunin mutane ukku, wato dalibai dake karatu a kasashen ketare da marasa lafiya masu bukatar zuwa asibitocin kasashen waje da kuma masu halartar taruka da yawon bude ido a kasashen ketare.
Wani da aka tambayeshi batun sabon shirin sai yace an ce za'a fara sayarwa amma ba'a fara ba saidai da alama zasu fara sayarwa din. Yace ko a wurinsu farashin dala ya sauko. Yace idan farashin dala ya sauka duk abubuwa zasu yi sauki a kasuwa.
Saidai cikin irin mutanen da aka lissafa za'a dinga sayarwa dala ba'a ambaci 'yan kasuwa masu zuwa kasashen waje sayo kayan da suke sayarwa a cikin kasar ba. Babu wanda ya san makomansu, ke nan har yanzu akwai sauran magana.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5