Fararen Hula dake Aleppo Na Cikin Mawuyacin Hali- MDD

Mutanen dake ficewa daga birnin Aleppo

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya ko MDD na musamman a Syria ya bada wani hasashe mai daga hankali a kan makomar birnin Aleppo a jiya Talata a yayinda fada ke kara zafi a birnin inda fararen hula da dama ke arcewa daga birnin.

Wakilin na MDD, Staffan de Mistura, yace wannan kaimi da sojoji ke karawa a wannan yaki, yana kyautata zaton yankin gabashin Aleppon ba zai yi karko ba.

Da yake jawabi a majalisar kasashen Turai, Mistura yace a kullu yaumi sojoji sai kara kutsawa suke yi zuwa cikin yankin.

Wannan kashedin ya biyo bayan munanan hare hare da sojojin gwamnatin Syriar ke kaiwa wanda ya tilastawa kimanin fararen hula dubu 16 arcewa daga gidajensu, kuma dubbai zasu bi sawu, a cewar MDD.

Kara zafi da wannan fada ke yi yasa fararen hula suna barin gidajensu babu komai a hannunsu kuma suna fadawa cikin wani halin fargaba inji jami’in bada agaji na MDD Stephen O’Brien.

Birtaniya da Faransa sun kira kwamitin sulhun MDD ya gaggauta shirya zama a kan wannan kisan kiyashi dake kara ta’azzara a jiya Talata ko kuma yau Laraba.

Jakadar Rasha a MDD Vitaly Churkin tace wannan kira da kasashen yammacin duniya suka yi, wata farfaganda ce kawai.