Majiyoyin jami’an tsaro sun ce Faransa ta tura sojoji tamanin a k’alla zuwa k’asar Jamahuriyar Nijer bayan an sace mutanen nan bakwai a makon jiya wadanda su ka had’a da Faransawa biyar da ‘yan wasu k’asashen Afirka biyu, wato d’an k’asar Togo d’aya, d’an k’asar Madagascar d’aya.
Majiyoyin sun ce sojojin Faransar sun kafa sansani a Niamey babban birnin k’asar Jamahuriyar Nijer, kuma su na ta shawagi ta jiragen sama a wani k’ok’arin neman gano inda ake yin garkuwa da mutanen bakwai.
Duka mutanen bakwai da aka sace dai ma’aikatan kamfanin nukiliyar k’asar Faransa ne na Areva. Ranar alhamis da ta gabata wasu mutane d’auke da bindigogi su ka sace su a garin Arlit da ke arewacin k’asar Jamahuriyar Nijer.
Faransa ta ce ta na zargin k’ungiyar al-Qa’idar arerwacin Afirka da shirya satar mutanen.
A can baya dai k’ungiyar ta sha fitowa fili ta d’auki alhakin aikata sace-sacen mutane,a ciki har da wani tsohon d’an k’asar Faransa mai shekaru 78 wanda ta sace a k’asar Nijer a cikin watan afrilu, kuma daga baya ta kashe shi.