Kasar Faransa na bukatar a yi wani taron gaggawa na Kwamitin Sulhu na MDD, don tattaunawa kan zargin sayar da wasu bakin haure ‘yan Afirka a matsayin bayi.
Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana hoton bidiyon al’amarin da gidan talabijin ta CNN ta nuna a makon jiya da “abin fallasa,” wanda kuma “ba za a lamunta da shi ba.”
“Wannan babban laifi ne ga dan’adam,” a cewar Macron bayan ganawarsa da Shugaban Kungiyar Tarayyar Afirka Alpha Conde. Ya kara da cewa, “Ina fatan za mu kara azama a yaki da masu safarar mutane wadanda ke aikata wannan danyen aikin, tare kuma da hada kai da dukkannin kasashen da abin ya shafa don wargaza su.”
Kafar ta CNN ta nuna hotunan bidiyon da ke nuna yadda ake cinikin wasu bakaken fata maza akan dala $400 kowanne, wadanda za a rika kai su gona su na aiki. Vidiyon ya janyo bacin rai a sassan duniya kama daga Turai zuwa Afirka.
Mai yiwuwa a yi taron na MDD a makon gobe, a cewar wani jami’in diflomasiyyar Faransa.