Rundunar ‘yan sandan kasar Faransa ta kama mutumin da ya dauki nauyin mayakan nan da su ka aikata kisan kiyashi kan dubun dubatan mutane a Rwanda a 1994.
Ma’aikatar Lafiyar kasar ta Faransa ta ce ‘yan sanda sun damke Felicien Kabuga a kusa da birnin Paris jiya Asabar, wato shekaru 26 bayan tsrerewarsa.
Dan shekara 84 din ya kasance mutumin da aka fi nema ruwa a jallo a kasar Rwanda kuma daya daga cikin na karshe cikin manyan wadanda ake zargi da hannunsu a kisan kiyashi ma mutane wajen 800,000 da su ka hada da ‘yan Tutsi da ‘yan Hutu da wasu masu tsattsauran ra’ayin kabilancin Hutu su ka aikata.
('Yan gudun hijirar yakin Rwanda, wanda su Kabuga su ka dau nauyi)
Kabuga, wanda ya taba kasancewa daya daga cikin mutane mafiya dukiya a Rwanda, an tuhume shi a 1997 da laifin kisan kiyashi baya wasu manyan laifukan kuma guda shida, kamar yadda ya ke a bayanin wata kotun kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya ta kafa.
Hukumomi sun ce Kabuga ya yi amfani ne da bayanin asali na karya wajen ba da sawu a Asnieres-Sur-Seine, arewa da birnin Paris, tare da taimakon ‘ya’yansa.
Kabuga, wanda dan kabilar Hutu ne da Amurka ta yi tayin tala miliyan biyar ga duk wanda ya bada bayanan da su ka kai ga kama shi, an yi zargin cewa ya bada kudin sayo dinbin adduna da kuma wasu kayan aikin gona wadanda aka yi amfani da su wajen aikata kisan kiyashin, a cewar wani dandalin yanar gizo na Majalisar Dinkin Duniya.