Macron Yace Yasan Illoli Tattare Da Mulkin Mallaka.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayinda yake ziyara a yankin New Caledonia, mai nemasn 'yancin kai.

Macron ya kai ziyara yankin ne dake kudancin tekun Pacific mai jama'a 270,000 dake shirin ballewa daga ikon Faransa a zaben raba gardama cikin watan Nuwamban bana.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron,ranar Asabar, ya amince da matsaloli dake tattare da "mulkin mallaka." Ya furta haka ne Asabar, yayinda ya kai ziyara yankin ko kasar da ake kira New Caledonia, a dai dai kuma lokcinda yankin dake kudancin tekun Pacific, yake shirin kada kuri'ar ballewa daga Faransa.

A karshen ziyararsa ta kwanaki uku, a Macron, yace Faransa, ba zata ci gaba zama yadda take ba idan yankin ya balle, sai dai yayi taka tsan-tsan na fitowa fili yayi kamfen na neman yankin su kada kuri'ar ci gaba da zama karkashin ikon Faransa.

Yankin dake gabashin Australia, yana da mutane da yawan su ya kai kusan dubu metan da saba'in, cikin su harda 'yan asalin yankin da ake kira kanaks,wadda yawansu ya kai kashi 40 cikin dari. Tuni dai yankin yake cin kwariya-kwariyar gashin kai, amma yana daga cikin muhimman wurare dake karkashin iko ko mallakar faransa, kama daga yankin Caribbean har zuwa yankin tekun India, da kuma sassa dake gabashin gabar ruwan a Canada.

Shugaba Macron, ya karrama 'yan kabilar ta Kanak su 19 masu gwagwarmayar neman 'yanci da aka kashe shekaru 30 da suka wuce, bayanda suka yi garkuwa da 'Yansanda a wani kogo a tsibirin da ake kira Ouvea yankin. Haka nan an kashe sojoji hudu a arangamar.