Fara Tayi Wa Manoman Junhuriyar Nijer Barna.

  • Ladan Ayawa

Kayan Amfanin Gona

Fara tayi wa manoma a Malbaza dake cikin jihar Tawa a junhuriyar Nijer mummunar barna, kuma maganin da ake kashe wadannan farin ya fara karewa

Rahotanni daga karkarar Malbaza dake cikin jihar Tawa a Junhuriyar Nijer sun bayyana cewa Manoma a yankin sun afka cikin iftilai’n fari.

Yanzu haka garuruwa 12 ne suka yi karo da wannan matsalar farin wadda tafi karfin maaikatar gidan gonar dake wannan yankin.

Haka kuma magungunan da akayi tanadi domin yaki da farar sun fara karewa ba tare da murkushe farar ba.

Umaru Duka na kauyen Lawe, daya daga cikin kauyukan dake fuskantar wannan bala’in, ya shaidawa wa wakilin Muryar Amurka, Sule Mummuni Barma cewa garuruwa kamar 15 ke fama da wannan matsalar.

Yace izuwa yanzu haka farar ta riga tayi mummunar barna ga gonakin jama’a.

Ga Sule Mummuni Barma da Karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Fara Tayi Wa Manoman Junhuriyar Nijer Barna.2'34