A jiya Lahadi ne Kungiyar wasan kwallon kafar mata ‘yan kasa da shekaru ashirin Falconets, suka fara wasan share fagen samun shiga gasar cin kofin duniya ta shekara mai zuwa wato FIFA 2016.
Inda suka lallasa abokan karawar su ‘yan wasan Laberiya da ci 7 – 1, a wasan su na farko a filin wasan Antoinette Tubman dake Monrovia.
‘yar wasa Adeboyejo ta jefa kwallaye 3 cikin raga a cikin mintuna goma sha biyar da fara wasan dai ta jefa kwallon farko, kafin Chinewendu Ihezuo ta jefa kwallo ta biyu cikin mintuna talatin a wasan.
Adeboyejo ta kara kwallo ta biyu wadda ta zamanto kwallon Najeriya ta uku kenan, bayan mintuna hudu ‘yan wasan Laberiya suka sami damar saka tilon kwallon su a raga, an dai tafi hutun rabin lokaci Najeriya na jagorantar wasan da ci 4 da 1.
Juliet Sunday ce ta jefa kwallo ta biyar a cikin mintuna 70 a wasan. Ita kuma Amarachi Ojinma ta jefa kwallayen biyun karshen da suka maida sakamakon wasan 7-1. Sai nan da makonni biyu masu zuwa Najeriya zata sake wasanta.