Babban limamin kirista na Katolika Fafaroma Francis ya fadawa dubban mahalarta taron matasa na duniya da aka yi Krakow ta kasar Poland da cewa, su yi ammana da sabon tsarin mutunta bil’adama.
WASHINGTON DC —
Da cewa kar su yi amfani da hanyoyi da kan iyakoki wajen tsana da shure bukatun neman daukin ‘yan gudun hijira.
Ya fadawa dimbin jama’ar da suka taru daga sassan duniya zuwa wannan taro na matasan duniya ne a wani katafaren fili.
A kuma rana ta karshe na kwanaki 5 din ziyararsa zuwa Kudancin Poland. Inda Fafaroman yayi kira ga duniya da su yi amfani da damar yadda duniya ta zama ta sadarwar yanar gizo.
Da cewa su dinga sauke manhajojin da zasu zama masu sadasu da ayyukan Alheri da tausayin juna to sadar da kyawawan dabi’u ba tare da tsana ko gajiyawa ba.
Ya kuma tabbatar da cewa taron matasan duniya na gaba a Panama ne nan da 2019 mai zuwa.