A jiya Talata 10 ga watan Maris ne sabon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadarsa dake birnin Tarayya Abuja, kwana daya bayan da gwamanatin jihar Kano ta nada shi a matsayin sabon Sarkin kano.
A saboda haka wasu ‘yan Najeriya ke ganin cewa Shugaba Buhari bai taka rawar da ya kamata ba don hana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje sauke Sarki Muhammadu Sanusi Lamido Sanusi na biyu daga sarautar Kano.
A wata hira da wakilin Muryar Amurka Umar Faruk Musa ya yi da Malam Garba Shehu, mai Magana da yawun fadar shugaban Najeriya, ya musanta wannan jita-jitar, ya ce Shugaba Buhari ya dauki duk matakan da ya kamata domin a yi sulhu ba tare da an yi nasara ba, bayan haka akwai batun dokokin kasa da ya zama wajibi a yi biyayya da su.
“Duk da cewa Buhari na da iko a matsayin sa na Shugaban kasa, bai kai ga ya hana Gwamnan wata jiha yin abinda dokar jiharsa ta ba shi ikon yi ba," a cewar Garba Shehu.
Ya kuma ce tun farko da batun sauke sarkin ya taso “an sa baki” amma aka fasa bayan da aka kafa wani kwamiti na gwamnoni 5 don su sasanta, a saboda haka bai dace ba wasu su ce Shugaba Buhari bai taka rawar gani ba wajen sulhunta bangaren masarautar da gwamnatin jihar Kano.
A nasa bangaren Alhaji Mohammed Lawal Kaugama mai sharhi kan lamura, ya ce ‘yan kasa sun sa ran Shugaba Buhari zai sa baki ya hana Gwamna Ganduje daukar matakin sauke Sarkin saboda karfin iko da daraja da kuma kimarsa. yana gani rashin sa bakin shugaba Buhari ya sa aka kai ga sauke sarki Sanusi.
Ga Karin bayani cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5