Fada ya zafafa a Sana'a baban birnin kasar Yamal a yau talata, ciki harda gidan shugaban wata kabila, wanda yake goyon bayan masu hamaiya. Sojojin gwamnati a birnin Sana'a sun kaiwa gidan Shekh Sadeq Al Ahmar hari. Rahotani sun baiyaa cewa dakarun yan tawaye sun samu nasarar mamaye gine ginen gwamnati da dama a birnin Sana'a.
Arangamomin sun nuna alamar wargajewar sasantawa tsakanin shugabanin kabilu da sojojin shugaba Ali Abdullah Saleh da aka bada sanarwarta a makon jiya. A halin da ake ciki kuma, jami'ai sunce wasu, wadanda ake zaton yan yakin sa kai ne sun kashe akalla sojoji biyar a birnin Zinjibar dake kudancin kasar. Sojojin gwamnati sun kaddamar da hari da jiragen saman yaki akan birnin bayan da a ranar lahadi yan yakin sa kai suka mamaye birnin.
Haka kuma shedun gani da ido sunce anyi arangama a birnin Taiz. Jiya litinin sojojin Yamal sun kashe fiye da masu zanga zangar ashirin a birnin Taiz. Shedu sunce sojoji sun bude wuta akan masu zanga zangar, suka kona tantuna sa'anan kuma suka lalata wani dakin shan magani, a lokacinda suke kokarin mamaye dandalin zanga zangar.