Yanzu haka shafin sada zumunta na Facebook ya tashi tsaye wajen ganin ya taimakawa mutane sun kare bayanansu a shafukansu.
A wani bangare na ranar tunatarwa game da kare bayanai a duniyar gizo, wanda aka ware duk ranar 28 ga watan Janairu, Facebook zai kaddamar da wani sabon shafi da zai taimakawa mutane su fahimci yadda zasu kare bayanansu a shafinsu na Facebook.
Facebook ya kirkiri sabon shafin ne ta yin amfani da sharhi ko bayanan da mutane suka rubutawa kamfanin, haka kuma ya hada kai da hukumomi da masana harkar tsaro a yanar gizo don samar da ingantacciyar hanyar da za a taimakawa mutane su fahimci yadda zasu kare kansu da bayanansu.
A kwai bayanai har 32 cikin yaruka 44 na duniya akan a shafin Facebook, da suka hada da batutuwa kan yadda mutum zai kare bayanansa, ya kuma sake salon tsarin mutanen da yake son su kalli abubuwan da ke shafinsa, da sauran hanyoyin ‘kara karfin tsaro.
Kaddamarwar dai ta zo ne a dai dai lokacn da mutane ke fargaba kan bayanansu da kuma al’amuran da suke gudanarwa a yanar gizo, Facebook ya dade yana fitar da hanyoyin kariyar bayanai don samarwa jama’a kwanciyar hankali.
Your browser doesn’t support HTML5