Yayin da katafaren kamfanin Facebook ke neman janyo hankulan sabbin masu amfani da shafinsa, ya sayi fitatciyar kafar sadarwar TBH, wadda take fitatciya ga matasa.
Abin da TBH ke nufi shine “To be Honest” a turance wato a Hausa kuma shine “a gaskiya” app din dai na baiwa matasa damar amsa wasu tambayoyin zabi ka tika akan abokansu, abokan kuma daga baya su sami sakamakon.
Sama da matasa miliyan biyar ne suka sauke app din TBH a wayoyinsu, inda suka aika da sama da sakonni Biliyan guda a ‘yan makonnin nan, a cewar kamfanin TBH.
Duk da yake dai wannan kafa tafi fice ga matasa, amma kowa na iya amfani da ita ba wai sai matasa kadai ba.
Wannan app dai na dauke da hanyoyin da mutane zasu iya yabawa junansu, wanda suka hada da tambayoyi irinsu ‘waye yafi kowa murmushi mai kyau?’ da ‘waye yafi baka dariya?’ duk wadannan domin samar da hanyar da matasa zasu sami karfin gwiwa akansu.
Facebook dai na ganin yana da alaka da kafar TBH ganin cewa baki dayansu suna kan tafarki guda ne, wato hada kan al’umma.
Your browser doesn’t support HTML5