A jiya Laraba ne kamfanin Facebook ya fitar da wani rahoto dake kunshe da matakan da ya dauka wajen kawo karshen ayyukan ta’addanci da hotunan batsa, kai harma da hotunan cin zarafin yara, da ake amfanin da kafofin yanar gizo.
Kamfanin ya tabbatar da rufe wasu shafuka fiye da biliyan 3.2, wadanda suka tabbatar da cewar shafukan karya ne, tun daga watan Afrilu zuwa watan Satumba, wanda ko a shekarar da ta gabata dai-dai wannan lokacin kamfanin ya rufe shafuka fiye da miliyan 1.5 na bogi.
Kamfanin ya kara da cewar ya saukar da sakkonin kiyayya, da tada zaune tsaye sama da miliyan 11.4, fiye da wanda yayi a shekarar da ta gabata da ya cire miliyan 5.4 cikin watanni shida a shekarar 2018.
Wannan shine karon farko da kamfanin na Facebook ya wai-wayi shafin rumbun hotuna na Instagram, inda ya ce an kafe hotunan yara da suke tsirara da ma na batsa sama da miliyan 1.2 wanda duk sun cire su.
Mai magana da yawun kamfanin Instagram Stephanie Otway, ta shaidawa gidan radiyon VOA cewar a can baya sashen Instagram nada wasu tsare-tsare na daban wajen bayanan sirri, da kuma matakan da ake dauka wajen ladabtar da duk wanda ya karya dokokin kamfanin.