Kamfanin Facebook ya bayyanar da cewar jiya Alhamis, ya rufe wasu shafufukan mutane sama da 800, wadanda mafi akasarin sun Amurkawa ne, da kuma sauran fadin duniya. Shafufukan dai suna da alaka da bayyanar da labarai da suka shafi siyasa, kuma basu da tushe na ire-iren labaran da suke wallafawa a shafukan nasu.
Kamfanin dai na Facebook, ya ki amsa tambayoyin da gidan radiyon VOA yayi masa dangane da shafukan da abun ya shafa, wanda ya hada da kimanin shafuka 559, da kuma wasu asusu 251, wanda wasu daga cikin shafukan ke adawa da manufofin shugaban Amurka Donald Trump.
Daya daga cikin shafukan da abun ya shafa a cewar kamfanin dillancin labarai na Washington Post, shafin nada masu bibiyar shi da suka kai fiye da mutane milliyan uku.
Shafukan na karya suna bayyanar da labaran karya, wanda mutane sukan bi shafukan daga nan sai ya kaisu cikin babban shafin su don ganin wasu tallace tallace, daga bisani mutun ba zai ga wani abun da yayi kama da labari na gaskiya ba.
Mafi yawan mutane sukanyi amfani da shafin na Facebook, wajen kara zuzuta wutar labaran karya ko wasu manufofin da suke son kaiwa gaba, harma wasu lokutta da dama sukan maida shafukkan nasu dandalin muhawa amma dukk acikin yaudara.